Sarakunan Gargajiya Sun Roki Hukumomi Su Kara Kaimi Wajen Daukar Matakan Samar Da Sassauci Ga Yanayin Kunci

Wasu sarakunar gargajiya

Yayin da tsadar rayuwa ta hanyar tashin farashin kayayyaki, musamman na masarufi ke karuwa a Najeriya, shugabannin sarautun gargajiya a kasar na ci gaba da rokon hukumomi su kara kaimi wajen daukar matakan da suka dace domin samar da sassauci ga yanayin kuncin rayuwa da talakawa ke ciki.

Wannan batu na magance tsadar kayayyaki da kalubalen tsaro da wasu sassan Najeriya ke fuskanta da kuma nanata muhimmancin hadin kai tsakanin al’uma na daga cikin manyan batutuwa da mai martaba sarkin Gaya a jihar Kano Alhaji Aliyu Ibrahim ya baiwa fifiko ya yin tattaunawa ta musamman da wakilan kafofin labaru na ketare a fadar sa, a wani bangare na murnar cikar sa shekaru biyu a gadon sarautar Gaya.

Alhaji Aliyu Ibrahim wanda aka nada sarki a ranar 27 ga watan Satumba shekara ta 2021 ya ce zaman lafiya da al’umma shi ne babbar nasararsa ta farko a gadon sarauta, yana mai cewa, an samu sauye-sauye da dama na ci gaba a yankin masarautar sa.

Sarkin ya ce hadin kai daga al’umma da ma gwamnati shi ne ginshikin wannan nasara.

“Mun samu hadin kai daga Jama’a mun samu hadin kai daga gwamnati, wannan irin hadin kai ne ya bamu damar sake gina babban masallacin Juma’a na garin Gaya, wadda al’umma a cikin da wajen masarautar gaya suka bada gudunmawa kuma za a yi bikin bude wannan masallaci a ranar Juma’a mai zuwa”.

Dangane da kalubale kuwa, mai martaba sarkin na Gaya ya ce duk kalubalen da ka ci karo dashi kuma ka sami sukunin warware shi ka ci nasara. “Kalubale bai wuce na kokarin shawo kan Jama’a ba akan al’amura, saboda yanayin dan Adam na banbancin fahimta da tunani kan lamura daban daban.”

Sai dai ya fayyace salo da tsarin daya bullo dashi domin karbar bayanai ko shawarwari daga al’umar masarautar sa, inda ya bullo da tsarin kafa kwamitoci akan fannoni daban daban kuma ta hanyar kwamitocin ne Jama’a ke gabatar da shawarwari da korafe-korafen su da akan tattaunawa a majalisar sarki domin daukar matakan da suka dace.

Yayin da sarkin na Gaya murnar cika shekaru 2 akan karaga, ya bayyana damuwa game da halin matsin rayuwa da al’uma ke ciki tare da kira ga mahukunta da mawadata a cikin al’uma su tallafawa tare da daukar matakan sassauci ga Jama’a.

“Jama’a lallai suna cikin wani hali, saboda haka muna kira ga gwamnati a matakai daban daban da kuma mawadata su kai agaji ga mabukata.”

Baya ga haka Sarkin ya hori al’umma su ci gaba da bada goyon baya ga shugabanni a dukkannin matakai da kuma addu’ar dorewar zaman lafiya da habakar tattalin arziki a kasa baki daya.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Sarakunan Gargajiya Sun Roki Hukumomi Su Kara Kaimi Wajen Daukar Matakan Samar Da Sassauci Ga Yanayin Kuncin