A wani taro da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umman suka gudanar a birnin legas shugabanin yankin yarbawa da kuma na sauran sassan Najeriya sun yi kira ga matasa da su kauracewa rikici a lokacin zabukan kasar dake tafe, tare da yin kira akan su fito domin kada kuri’a.
Oba Hammed Adekunle Makama, shine basarake ko Olowu a jihar Osun wanda kuma ya jagoranci taron sarakunan a birnin Legas. Dage zaben kasa da akayi na mako guda ya sanya wasu matasa da kuma sauran masu zabe barazanar kauracewa zaben na ranar asabar.
Shima a bangaren sa sarkin fulanin Legas Alhaji Muhammadu Banbado, yayi bayani game da zaman lafiya tsakanin al’umomin Najeriya dabam dabam musanmman a wannan lokaci na zabe yanzu, domin karawa masu zaben kwarin guiwa.
Yanzu haka gwamnati ta ayyana ranar juma’a a matsayin ranar hutu, kana kuma wasu kanfanonin jiragen sama da masu motocin haya sun ayyana rage kudaden sufuri domin bada goyon bayan ga masu zabe sake komawa garuruwan su domin zabe.
Haka ita ma gwamnatin tarayya da wasu gwamnatocin jihohi sun umarci biyan albashin ma’aikata duk dai domin.
Ga karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5