Sarakunan Gargajiya a Accra Sun Yabawa Muryar Amurka Yayin Da Ya Cika Shekaru 45 Da Kafuwa

Sarakuna gargajiya na al’ummar Zango dake Accra babban birnin Ghana

Dokta Lamido Jibril Sissy, sarkin yankin Gbawe da kewaye, kuma tsohon jami’in yada labarai ne a GBC Ghana, da kuma sashen Hausa na Muryar Jamus yace babu shirin dake burge shi kamar Tsaka Mai Wuya domin yadda ake gabatar da shirin.

Yayin da sashen Hausa na Muryar Amurka ke bukin cika shekaru 45 da fara watsa shirye-shiryenta, Sarakuna gargajiya na al’ummar Zango dake Accra babban birnin Ghana, sun yabawa tashar bisa kyakkyawar tasiri da take yi ga al’ummarsu, ta hanyar sanar da su ababan dake gudana a duniya, da ilmantarwa da kuma nishadantar da su, a harshen da suke fahimta.

Dokta Lamido Jibril Sissy, shi ne sarkin yankin Gbawe da kewaye, kuma tsohon jami’in yada labarai ne a GBC Ghana, da kuma sashen Hausa na Muryar Jamus.

Sarki yace babu shirin dake burge shi kamar Tsaka Mai Wuya domin yadda ake gabatar da shirin.

"Shirin nan na Tsaka Mai Wuya, shiri ne mai kayatarwa. Sunan shirin ma da kansa yana da daukar hankali; idan ma baka san ma’anar sunan shirin ba, kafin an gama za ka fahimta."

Aliyu Mustapha Sokoto

Shugaban sarakunan Fulanin Ghana, Sarki Alhaji Idrisu Muhammed Bingel, ya taya sashen Hausa murnar cika shekaru 45. Yace, ya fara sauraron Muryar Amurka tun lokacin da aka fara shirye-shiryen Hausa a tashar, tun suna kan gajeren zango har zuwa yau.

Shirin Lafiya Uwar Jiki da shirin A bari Ya Huce na daga cikin shirye-shiryen dake burge shi..

Sarkin zangon Kwashiman, Imurana Billa Ango ya jinjinawa Muryara Amurka da fatan alheri, ya kuma nuna cewa yana son duk shirye-shiryen da sashen Hausa na Muryar Amurka ke gabatarwa. Domin haka, a duk lokacin da rediyon mahaifinsu ya lalace, suna kokari ne su gyara kafin lokacin VOA ya kai.

Ya kara da cewa"da an yi sallar asuba, to ya kamata ya kasance a gaban rediyo. Muna yi musu fatan alheri da kuma fatan Allah Ya kara musu hikima wurin gabatar da shirye-shirye."

Alhaji Salisu Maude, Sarkin Samarin Hausawan Accra, yace Muryar Amurka ta taimakawa al’ummar Zango ta bangaren samun labarai da ilmantarwa, haka kuma tashar ta taimakawa masu magana da harshen Hausa a Ghana gyara Hausarsu.

Yace, yana son shirin Nakasa Ba Kasawa ba da Zauren Matasa, domin yana samun hikimomi a matsayinsa na Sarkin Matasa.

Saurari rahoton Idris Abdullah a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Sarakunan Gargajiya a Accra Sun Yabawa Muryar Amurka Yayin Da Ya Cika Shekaru 45