Sarakunan gargajiya da masu fada a ji tsakanin al’umma suna ci gaba da bada goyon baya da hadin kai a yunkurin shawo kan mace macen kananan yara.
Shugabannin al’umman sun bayyana goyon bayansu ga shirin rigakafin ne a wani taron karawa juna sani da ya hada kan iyaye da masu ruwa da tsaki da nufin fadakar da al’umma kan illar kin amincewa a yiwa ‘ya’yansu rigakafin cututukan nan shida dake katse hanzarin kananan yara.
Taron da aka gudanar a Maiduguri jihar Borno shine na uku bayan wanda aka gudanar a birnin Ikko da kuma jihar Nassarawa.
A cikin jawabinshi, ko’odinetan kungiyar wayar da kan jama’ar ya bayyana cewa, sakacin iyaye ne yake kai ga rasa rayukan kananan yara, kasancewa, iyaye da dama basu tashi kai ‘ya’yansu asibiti sai cuta taci karfinsu duk da yake an shirya rigakafi da ake ba kananan yara kyauta daga lokacin haihuwa har zuwa shekaru biyar.
Bisa ga cewarshi, hakan na faruwa ne sabili da rashin fahimtar muhimmancin rigakafin.
Mai martaba Shehun Borno Alh Garba Ibn Elkanemi, wanda ya yi magana ta bakin Alhaji Mala Garba yayi kira ga jama’a da su rika bada goyon baya ga shirin allurar rigakafi, kasancewa a matsayinsu na iyaye suna da haki kan ‘ya’yansu.
Mallam Sa’adu Gabdu wani malamin addinin Islama a jihar Borno ya bayyana matsayin allurar rigakafi a addinin Islama inda yace Musulunci ya yarda da allurar rigakafi sabili da haka babu hujjar kin yiwa kananan yara rigakafin.