Fauziyya Idris Garkuwa – matashiya mai sana’ar zanuwan gado. Tana dinka zannuwan gado dake cike da auduga da wadanda ma ba’a sa musu auduga, bargo da wasu kayan kyalkyali na kawata gado.
Ta kan saro yaddukan zanuwan gadon ne a kasuwar kofar Wambai dake Kano Najeriya, inda take dinka su, ta ke sayar da su ga mabukata.
Tana gudanar da wannan sana’a ta ta ne, ta hanyar tallata kayan ta kafofin sadarwa na zamani, inda ta ke sanya kayan na ta wa mabukata su gani, su kuma nuna sha’awarsu domin su saya.
Babban abinda ya ja hankalinta ga kananan sana’o'i, a ta bakinta, domin ta zama mai dogaro da kai ne, duk kuwa da cewar tana karatu a jami’ar Bayero ta Kano, a lokacin da ta fara sana’ar ta, kuma ta lura da cewar ana samu kudaden kashewa ta hanyar sana’ar hannu.
Ta ce ta fara da naira dubu goma a wancan lokacin, a yanzu kuwa a sati guda takan dinka zannuwan gado daga goma zuwa goma sha daya. Ta kara da cewa ta fara harkar kasuwanci ne da wuya da jajircewa, amma sai kasuwa ta bude.
Daga cikin kalubalen da ta fuskanta a lokacin da ta fara sana'ar, sun hada da wajen saro kayan. Akan samu hau-hawan farashi wanda mai saye baya la’akari da hakan, da zarar an kara masa farashi sai ya fara korafi.
Daga karshe ta shawarci mata da su jajirce wajen neman sana’a, tare da ja musu hankali da kada a raina sana’a komin kankantarta, da sannu ake kafa sana’a har ta bunkasa a kuma ci riba a gaba.
Your browser doesn’t support HTML5