A yayin ziyarar, ‘yan majalisar sun nuna takaicinsu game da irin asarar rayuka da kuma dukiyar da aka yi cikin ‘yan kwanakin nan sakamakon tashe-tashen hankula a yankin karamar hukumar Lamurde da ke kudancin jihar Adamawa.
Kauyukan da tashe tashen hankulan suka faru sun ko hada da Gon, Bolki, Mbemun da kuma garin Tingno, inda nan aka fi asarar rayuka da kuma dukiya.
Da ya ke jawabi ga al’ummomin yankunan, dan majalisar dattawa da ke wakiltar mazabar Adamawa ta kudu Sanata, Binos Dauda Yaroe ya ce manufar ziyarar ita ce don ganin abubuwan da suka faru tare da bada tallafin abinci ga wadanda lamarin ya shafa.
Dan majalisar wanda ya ce tuni majalisar dattawa ta umarci hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya wato NEMA da kuma hukumar raya arewa maso gabas da ake kira NEDC a takaice, da su kai agaji. Ya kuma ce zasu ci gaba da bibbiyar lamurran da ke faruwa tare da bada hadin kai ga jami’an tsaro domin ganin ba a sake samun tashe-tashen hankulan ba.
Da suke jawabi, wasu shugabannin al’ummomin da tashe-tashen hankulan suka shafa, sun nuna takaicinsu game da abubuwan da ke faruwa tare da yin kira ga gwamnatin jihar da ta kafa kwamitin bincike da sasantawa domin maido da zaman lafiya.
Ita ma Hajiya Kaltume Abdullahi Abari shugabar kungiyar mata musulmi ta Najeriya wato FOMWAN a jihar Adamawa, da su ma suka je jajanatawa jama’ar ta yi kiran sasantawa.
Wannan dai na ko zuwa ne yayin da gwamnatin jihar Adamawa ke kafa wani kwamitin bincike kamar yadda Mr. Solomon Kumangar da ke zama daraktan yada labaran gwamnan jihar ya shaida.
Saurari cikakken rahoton daga Ibrahim Abdul'aziz:
Your browser doesn’t support HTML5