Yayin da gwamnatin Najeriya Najeriya ke cigaba da zafafa kokarin kwato kudaden da aka ware a baya don yaki da ‘yan Boko Haram daga wajen wadanda ake zargin sun handame, Majalisar Dattawan kasar ta ce ta na goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari, kan matakin da ya ke daukawa na farauto kudaden saboda a dakile Boko Haram da sauran matsalolin tsaro don talaka ya samu ya dan sarara.
Shugaban Kwamitin Ayyukan Musamman Na Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Abdul’aziz Murtala Nyako ne ya tabbatar ma menema labarai hakan a Yola, hedikwatar jahar.
To saidai kuma ba a taru aka zama day aba, saboda akwai kuma masu caccakar matakan da ake daukawa na kwato kudaden daga wadanda ake zargin sun wawuren.
Ga dai wakilinmu Ibrahim Abdul’aziz da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5