Bisa ga yadda suka fahimci sakowar 'yan matan Chibok, Sanata Ali Ndume ya yiwa Allah godiya da gwamnatin shugaba Buhari da jami'an tsaro da gwamnatin jihar Borno da gwamnatin kasar Switzarland da kungiyar agaji ta Red Cross da yawancin kungiyoyin sa kai da suka taimaka.
Sanata Ndume yayi fatan sauran 'yan matan Chibok din da har yanzu suke hannun Boko Haram su ma za'a sakosu. Abun da ya faru shi ne suke ta yin addu'a a kai yau shekara uku amma lokacin da Allah ya kaddara ya fi, injishi. Ya yabawa gwamnatin Buhari da wannan namijin kokari da tayi.
Dangane da cewa an samu sa bakin wata kasar waje da ma kungiyoyin kasa da kasa, Sanatan yace ba wani sabon abu ba ne. Dama idan an samu rigima a koina yawancin lokuta kasashen waje su kan shiga tsakani su kawo daidaito.
Akan korafin da wasu su keyi domin an yi musayar 'yan matan da 'yan ta'adda Sanata Ndume yace shi bai da cikakken bayanin abun da ya faru. Amma musaya da 'yan ta'adda shi ma ba sabon abu ba ne. Yace ko Amurka ma kwana kwanan nan tayi suyan 'yan ta'addan da take rike dasu a Gontanamo domin a sako mata sojinta da 'yan ta'addan ke garkuwa dashi. Israila ma ta sha yin musayan 'yan ta'adda akan gawarwakin sojojinta ma, inji Sanata Ndume.
Game da sauran 'yan matan fiye da dari da har yanzu suna tsare Sanata Ndume yace fatansu shi ne gwamnati ta kara himma da kokari domin a sakosu. Yana mai cewa sauran iyayen da ba'a sako 'ya'yansu ba damuwarsu zata karu.
Sanatan ya taya garin Chibok murna tare da kiran a cigaba da addu'a.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5