Tallan Zogale Tasani Sha'awar Makaranta

Talla a Arewacin Najeriya

Sana'ar talla na daya daga cikin abubuwan da mutanen karkara suka fi baiwa muhimmanci, kuma wannan na daya daga cikin dalilan da ke haifar da wasu matsaloli musamman ga 'ya'ya mata.

A hirar da wakiliyar Dandalin VOA Hausa Baraka Bashir ta yi da wata yarinya mai shekaru goma sha shidda, wadda ke tasowa tun daga Kauyen Kumbotso na jahar Kano zuwa cikin gari domin tallara zogala da albasa, ta nuna cewar mahaifiyar ta ce ta ke dora mata wannan sana'a kuma hakan bai hana ta zuwa makaranta domin neman ilimin boko ba.

Amma abin dubawa anan shine, wacce irin gudummuwa iyaye a karkara suke badawa domin ba 'ya'yan su ilimin boko?.

A'isha ta nuna cewar duk da wannan sana'a ta tallar zogala da albasa da mahaifiyar ta ke dora mata, tana samun lokacin zuwa makarantar boko kuma a yanzu haka tana aji hudu na makarantar firamare, kuma ta kara da cewar fatan ta a rayuwa shine idan ta gama makaranta duk abinda Allah ya hore mata shi zata yi.

Daga karshe matashiyar ta ce "ina so inyi ilimin boko kwarai da gaske dan haka nake zuwa tallar kuma ina bada kokari domin zuwa makarantar haka nan."