Wata matashiya kuma malamar makaranta mai suna Hauwa Garba Ahmed, ta zanta da wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir inda ta bayyana mata cewa bayan koyarwa da ta keyi tana kuma yin sana’ar yiwa mata kwalliya domin suyi kyau.
Tun tana karamar yarinya Hauwa tana da sha’awar yiwa ‘yan mata kwalliya, yanzu haka ma da ta girma ta kuma zama malamar makaranta bata bar sha’awar yiwa mata kwalliya ba, zama malamar makaranta bai hana ta samun lokacin bude sabuwar sana’ar mai da tsohuwa yarinya ba, inda take yiwa duk ‘yan mata da amare kai har ma da duk wanda ke bukata.
Burin malama Hauwa shine ta saka mutane suyi kyau musammam ma in suka duba madubi suyi murmushi, kafin ta mai da yin kwalliya sana’a ta ‘dauki shekaru biyar tana yiwa ‘yan uwanta da abokan arziki kwalliya, tana zuwa gidajen mutane tayi musu ko kuma mutane su zo har gidan ta domin tayi musu kwalliya.
Kalubale ‘daya da take fuskanta shine mutane na daukar wannan sana’ar ta kwalliya a matsayin wani abin wasa, suna ganin kamar kowa ma zai iya. Tayi kira da mutane da su girmama sana’a duk ‘kankantar ta a rayuwa. Ita dai burinta shine ta yi wa amare da ‘yan mata kwalliya su fito suyi kyau.