Sana'ar Dogaro Da Kai Abin Alfahari Ce

Rashida Tsakuwa

An ja hankali matasa da su jajirce wajen dogaro da kai domin neman nasu na kansu ganin cewa ba komai bane Gwamnati zata yiwa mutane duba da ganin yadda tattalin arzikin duniya yake.

Wata karamar ;yar kasuwa Rashida Tsakuwa, ce ta furta haka a wata tattaunawa da wakiliya Dandalinvoa Baraka Bashir.

Kasance bashi na daya daga cikin kalubalen da masu sana’a ke fuskanta Rashida tace ita bashi baya kashe mata gwiwa wajen fasa sana’ar da take yi- inda take cewa a yanzu haka tana dinka kaya ne tana kaiwa kasar Saudia.

Ta ce ta faro ne da sana’ar saka , sannan ta koma na dinkin duk a zumar share wa kanta hawaye tare da magancen kanana da manyan matsalolin rayuwa kasancewar ba ta sami damar karatun boko ba.

Ta kara da cewa tana sana’ar ne gudun kada ‘yayanta su kasance masu sa ido a abuinda akewa wasu yara batare da ta iya yi masu duk abinda suke bukata ba.

Malama Rashida ta ce, matsalolin gidan miji na daya daga cikin abinda ya sa ta fara sana’a ta ce gudun kada ta tambaya a ce babu ko a hana ta, ta fara sana’arta kuma a yanzu tana sana’ar hajja da suka hadar da kayayyakin sutura, da sauran kayayyakin mata har da na maza

Ta kara da cewa sana’ar ta yi mata komai, da sana’arta ta sami damar kai iyayen ta Makkah domin sauki farari ta yi gida nata na kanta da ma sauran kadarori.

Your browser doesn’t support HTML5

Sana'ar Dogaro Da Kai Abin Alfahari Ne - 4'30"