Hajiya Fauziya Muhammad, mai masana’antar Fauzy, inda ta ke koya wa mata sana’ar dogaro da kai ta dinki ta ce Ganin cewa a lokacin da ta bude wannan masana’anta ba’a cika samun mata masu shagunan dinkin da ake koyawa mata ba hakan ne ya sa ta samu mutane da dama wadanda suke zuwa domin a koya musu dinki.
Ta ce a duk sana’ar da mutum zai yi dole sai ya fuskanci kalubale musamman ma kasancewarta mace, ta kara da cewa ta gaji sana’ar dinki ne a wajen mahaifiyarta
Malama Fauziya ta kara da cewa kimanin shekaru ashirin da biyar Kenan da ta fara sana’a dinki ana kuma biyanta ta ce ta shafe shekaru 15 kenan tana koyawa mata kananan sana’oi inda take cewa bayan ta kammala karatun ta na digiri ne ta ga cewar ba zata iya aikin ofis ba illa sana’ar hannu kamar yadda ta saba tun kafin ta kammala karatunta.
Daga cikin hanyoyin da mace zata bi kafin ta dauki mace don ta koya mata sai maigidanta ya zo neman izini kafin a fara koya mata haka nan ma idan budurwace sai iyayenta sun nemi izini, daga bisani aka bata shawara ta fitar da form da mace zata saya kafin a fara koya mata aiki.
Daga karshe ta ja hankalin mata da su tashi domin neman nasu na kansu inda take cewa da zarar mace na sana’ar hannu toh ba ita ba matsalar aure tsakanin ta da mijinta, ta kara da cewa a mafi akasarin matsalolin da ake samu tsakanin ma’aurata baya wuce na bani-bani da rashin abin yi a gidan miji.
Daga cikin matan da Hajiya Fauziya ta yaye a wannan karo akwai Zainab Usman, wadda ta ce ta shafe shekaru 9 kenan tana wannan harka ta dinki, ta ce wannan shine karo na biyu da ta karbi takardar shaidar kammala koyon sana’a. A cewarta samun mace mai jajircewa irinta sai an tona.
Ita kuwa Hindatu Hassana ita ma kamar Zainab, yabawa tayi da kokari Hjiya Fauziya tace da cewar farin cikinta ba zai misaltu ba kuma ta ja hankali mata da su dage wajen neman sana’ar hannu tare da cewar sai an daure ake kai ga nasara.
Your browser doesn’t support HTML5