Sana'a Ce Kadai Hanyar Kauda Takaicin Yau Da Gobe- Inji Maryam Idris

Ina sayar da kayayyakin da suka danganci mata, kama daga atamfa ko mayafai da sauransu, maganin zaman banza da magance kananan bukatu inji malama Maryam Idris.

Ko da ya ke wannan sana’a dai baya ga magance matsalolin gaba tana tattare da wasu matsaloli na rashin biyan bashi wanda hakan ke kawo tsaiko ga kasuwanci a wasu lokutan.

Matashiyar ta ce, a mafi yawancin lokuta saboda sana’ar ce ta sa mata masu kananan sana’oi basa kosawa amma harkar a cewarta na da sarkakiya da dama duk kuwa da cewar masu iya Magana kan ce sana’a goma maganin mai gasa

Malama Maryam ta ce sana’a abin yi ce ko da kuwa namiji ya hana mace karatu ko aiki, sana’a ce kadai hanyar da za’a kauda takaicin yau da gobe.