Gasar karni na 21 bai wuce samarwa da inganta yanar gizo a duniya ba, ko da kuwa jirgin saman nan ne mai zuwa duniyar wata da ya shahara SpaceX da kamfanin Amazon, basu kai samar da yanar gizo a kauyuka na fadin duniya ba.
Kamar karni na 20 lokacin da tarayyar kasashen kungiyar Soviet Union ta kaddamar da na’urar tauraron dan Adam a duniyar wata, a shekarar 1957. Gwammar kamfanonin Amurka sun gabatar da bukatar su ga hukumomin don basu damar harba wata na’urar tauraron dan Adam zuwa duniyar wata.
Hakan zai bada damar samar da yanar gizo ga duk wasu kauyuka da suke cikin sunkurun daji. Duk inda hasken rana yake to babu shakka za’a samu yanar gizo cikin sauki, idan har wadannan kamfanonin sun samu damar aika wannan tauraron.
Babban burin shine samar da yanar gizo a ko’ina a fadin duniya, a cewar shugaban kamfanin Amazon Jeff Bezos, ya kuma kara da cewar kimanin rabin mutane a duniya da suka kai biliyan 3 basa amfani da yanar gizo, rashin yanar gizo na maida harkokin kasuwanci baya, kana yara basu samun damar yin aikin gida da akan bada daga makarantu, akwai bukatar samar da yanar gizo a fadin duniya don samun dai-daito a al’amurran yau da kullun.