Kamar yadda alkalumma ke nunawa baya ga rayukan makiyaya,kawo yanzu sama da shanu dubu 70 ne suka salwanta sanadiyar rikicin Boko Haram a jihohin Adamawa,Borno da kuma jihar Yobe,lamarin da yanzu ya jefa makiyaya cikin halin ni yasu.
Baya ga rayukan da aka rasa sakamakon rikicin na Boko Haram da aka shafe fiye da shekaru bakwai ana fama da shi, wani nau’in da wannan rikici ya fi shafa shine na rayukan makiyaya da kuma dabbobinsu.
A wajen wani taron manema labarai da hadakar kungiyoyin makiyaya a Najeriya suka kira ,shugabanin kungiyoyin sun koka ne da cewa an maida su saniyar ware.
Alh.Alkali Bello Wazirin Madagali dake zama shugaban kungiyar Fulani ta Weti Weli a Najeriya, ya ce rikicin Boko Haram ya lukume rayukan Fulani makiyaya da dama baya ga na shanu da sauran dabbobi.
Haka shi ma Alh. Abdu Bali shugaban kungiyar Tabital –Puulaku Njode-Jam a Najeriya,ya ce yanzu haka akwai mata da yara da dama da rikicin Boko Haram ya jefa cikin mawuyacin hali.
Shugabannin sun yi kiyasin cewa akalla shanu sama da 70,000 ne suka salwanta saboda rikicin na Boko Haram.
Wannan korafi na zuwa ne yayin da al’ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa ke zargin cewa ana karkatar da kudaden ayyukan kwamitocin da gwamnatin kasar ta kafa domin tallafawa wadanda hare –haren Boko Haram ya shafa.
Su dai hukumomin da ake zargin sun sha musanta wannan wanna zargi.
Your browser doesn’t support HTML5