"Sama Da Mutum Miliyan 100 Ba Su Da Aiki Mai Tsoka a Najeriya"

A Najeriya, Kiddidiga da ma'aikatar Kwadago ta yi, ta nuna cewa, a cikin mutanen kasar Najeriya miliyan 200 da ake da su, sama da miliyan 100 ba su da aiki mai tsoka da zai iya fitar da su daga kangin talauci.

Hakan na nufin, cewa kashi 60 cikin100 na daukacin mutanen kasar abin ya shafa.

Amma Ministan ma'aikatar ba da agaji, walwala da jin dadin jama'a, Sa'adiya Umar Faruk, ta tabbatar wa Muryar Amurka cewa, gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, na aiki tukuru wajen tabbatar da cika alkawuran da ta yi na fitar da mutane miliyan 100 daga kangin talauci.

Mutane Sama Da Mliyan 100 Basu Da Aiki Mai Tsoka A Najeriya

Ta kara da cewa, ba za'a samu wannan nasara cikin gaggawa ba, amma ta ce suna daukan matakan da za su taimaka wajen cimma wannan buri, kamar sha'anin tsaro da tace tsoffin 'yan boko haram, domin su shiga ayyukan taimaka wa kansu da kasa baki daya.

'Yan Najeriya da dama, kan yi korafin rashin cika alkawarin da 'yan siyasa ke yi, musamman wadanda suka yi a lokutan yakin neman zabe.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

"Sama Da Mutum Miliyan 100 Ba Su Da Aiki Mai Tsoka a Najeriya"