Sama Da Mutane Miliyan Daya Ke Ba Haya A Fili A Najeriya:UNICEF

Wani yaro yana ba haya a fili

Asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya yace 'yan Najeriya miliyan 47 ne wato kashi 24 cikin dari ke bayan gari a fili ko a makewayi marar inganci a binciken data gudanar a shekarar 2018.

UNICEF ta bayyana hakan ne a lokacin taron manema labarai da aka gudanar a jihar kano kan batun tsaftar muhalli ta hanyar yaki da bayan gari a fili.

Dangane da wannan lamarin, mataimakin daraktan bincike da sa ido na ma'aikatar kula da muhalli na Abuja Hassan Abubakar yace wannan dabi'ace marar kyau wadda tu'ammali da miyagun kwayoyi ke haifar wa, kuma ma'aikatar na hukunta duk wadda aka samu yana aikata hakan.

Shima a nashi bayanin, jami'in tsafta na ma'aikatar kula da muhalli a Abuja Simeon Ajueyitsi yace suna fuskantar karancin baddaki na jama'a a birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Dakta Lawal Musa Tahir wani likita da Sashen Hausa ya yi hira da shi dangane da batun yace ba haya a fili na kan gaba wajen yaduwar cututtuka kamar amai da gudawa, zazzabin Tyhoid, ciwon hanta da sauran su.

Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin kokarinta don ganinan kawo karshen bayan gari a fili zuwa shekara ta 2025.

Saurari cikakken rahoton Hauwa Umar

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Najeriya da dama suna ba haya a waje-2:57"