Sama Da Mutane 150 Sun Rasu Sakamakon Girgizar kasa a China

Girgizar kasa a China

Wata girgizar kasa mai karfi da aka yi a kasar China tayi sanadin mutuwar sama da mutane 150 yayinda sama da dubu uku kuma suka ji raunuka
Adadin wadanda suka rasu a gagarumar girgizar kasar da aka yi a yankin Sichuan dake yammacin kasar yau asabar da safe ya haura zuwa sama da dubu dari da hamsin, yayinda sama da mutane dubu uku suka ji raunuka.

Kamfanin dillancin labaran kasar China Xinhua yace shugaban kasar China Xi Jinping ya umarta daukar dukan matakan ceto mutane domin rage yawan wadanda zasu rasa rayukansu sakamakon bala’in.

Hukumar tantance karfin girgizar kasar ta Sichuan tace karfin wannan girgizar kasar ya kai maki 7.0 yayinda takwararta ta Amurka ta tsaida ta a kan mai karfin maki shida da digo shida, wadda ke iya haddasa barnar gaske. Nisanta a karkashin kasa kuma ya kai kimanin kilomita goma sha biyu.

Kamfanin dillancin labaran kasar china Xinhua yace girgizar kasar ta jijjiga gine gine a babban birnin Lardin Chengdu dake tazarar kilomita 115.

An yi girgizar kasa mai karfi a Sichuan cikin shekara ta dubu biyu da takwas da tayi sanadin mutuwar sama da mutane dubu saba’in.