Sama Da Matasa 200 Sun Ajiye Makamansu a Garin Maiduguri

Wata kungiyar ci gaban al'umma da hadin kan jama'a da ake kira “Yarwa Community Development Association” dak e Maiduguri a jihar Borno, ta fadakar da wasu matasa su 236 akan illar aikin ta'addanci da kuma bangar siyasa akan jama'a, wanda hakan ya sa matasan daukar matakan zaman lafiya tare da ajiye makamansu.

Matasan sun fito daga yankunan Gomari, Binta Suga, Jambawa da Bulumkutu kasuwa, da dai sauran wasu bangarori a karamar hukumar Jere, inda suka mika makamansu ga hukumomi sakamakon zaman fadakarwar da kungiyar ta yi da su.

Shugaban kungiyar Alhaji Muhammad Buddu Hasaan ya ce, sakamakon tashe-tashen hankulan da ake yawan samu a yankunan ya sa kungiyar ta gayyaci matasan tare da fadatar da su akan illar ta’addanci da yawan tashe-tashen hankula, tare da nuna musa muhimmancin zaman lafiya da ci gaban al’umma.

Saurari Karin bayani cikin sauti daga Haruna Dauda Biu.

Your browser doesn’t support HTML5

Sama Da Matasa 200 Sun Ajiye Makamansu a Garin Maiduguri