Sama Da Mata Dubu 10 Masu Yoyon Fitsari Aka Yi Wa Tiyata a Jos

Taron mata masu yoyon fitsarin da aka yi wa tiyata a jos

Cibiyar tallafawa masu larurar yoyon fitsari dake a Asibitin Jankwano a Jos, ta ce ta gudanar da aikin tiyata ga mata fiye da Dubu 10, kuma dukkansu suna cikin koshin lafiya.

A bikin ta na shekara-shekara da ta ke tattaro dukkan wadanda aka yi musu tiyata a cibiyar, don yin zumunci da juna da ‘karfafa masu yoyon fitsarin gwiwa. Likitan da ke kula da marasa lafiyan Sunday Lengman, ya ce cibiyar na samun ci gaba da taimakon tuwaran mishan da wasu kungiyoyi.

Dakta Sunday ya ce cibiyar ta dade tana taikawa mata masu fama da matsalar yoyon fitsari har sama dubu 10, haka kuma cikin matan da aka yiwa aikin akwai wasu sama da 300 wanda suka sami juna biyu suka dawo cibiyar ta sake yi musu aikin fida domin su haihu ba tare da matsala ba.

Haka kuma cibiyar ta taimakawa kasahen Afirka 15 da sauran wasu kasahen duniya, ta hanyar koyar musu da wannan aikin tiyatar yoyin fitsari.

Wannan cibiya dai na samun taimakonta daga gurare daban-daban, don ci gaba da taimakawa mata masu yoyon fitsari da aikin tiyata kyauta ba tare da sun biya kudi ba.

Taron mata masu yoyon fitsarin da aka yi wa tiyata a jos

A cewar likitan da ya fara kafa cibiyar shekaru 25 da suka gabata, Steve Smith, lokacin da ya fara aiki a cibiyar matan da ke zuwa basu da kudi kuma ‘yan uwansu sun watsar da su. Hakan yasa ya gayawa ‘yan uwansa a Amurka su taimaka da kudade don yi musu aiki.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Sama Da Mata Dubu 10 Masu Yoyon Fitsari Aka Yi Wa Tiyata a Jos - 3'59"