Yayin da ya rage kasa da mako guda daya kafin karamar Sallar, 'yan kasuwa da jama'ar gari musamman talakwa sun fara kokawa bisa tsadar suturun da za su saka a lokacin bukukuwan sallah karama.
A babbar kasuwan Kumashi da ke Ghana wasu mutane da suka zanta da Muryar Amurka, sun nuna damuwa kan tsadar kayayyakin sakawa.
Wata mata mai suna Maami da ke sayar da takalma a bakin kasuwar Kumashi ta ce farashin takalma ya ninka har sau biyu in aka kwatanta da na bara.
Shi kuwa Mallam Misbawu mai kawo hulluna da shaddodi daga Kano a'arewacin Najeriya ya tabbatar da tsadar sutura a bana yana mai cewar shigowa da kaya da wahala a wannan karo abin da ya yi sanadiyar tashin kudin kaya kenan.
Hajia Ramatu 'Mr. and Lady Boutique' daya daga cikin manyan 'yan kasuwa a Ghana masu kawo sutura daga manyan kasashen larabawa da Najeriya tare da China ta alakanta tsadan kaya a bana bisa faduwar sidi idan aka kwatanta da dalar Amurka.
Farfesa Nail Muhammad Kamil babban lakciran ilimin kasuwanci a Jami'ar kimiyya da fasaha ta "KNUST" ya ce mamayar da Rasha ke yi aUkraine na ta'asiri sosai akan farashin kayayyaki.
Mallam Musah Shekayi, daya daga cikin masu magana da yawun gwamnati, ya ce na daga cikin matakanda suka dauka shine gwamnati ta bude iyakokin kasar tareda zuba zuzurutun miliyoyin dalolin Amurka domin karfafa Ghana sidi.
A karon farko tun shekarar 2009 Ghana ta fuskanci hauhawan farashin kayayyaki da ya kai kashi 19.4 a watan Maris din bana da ya daidaita da azumtan watan Ramadana.