Yayin da ya rage sauran kwanaki kadan a gudanar da bikin sallah Majalisar Koli kan harkokin addinin Islama ta NSCIA a Najeriya ta yi wa mutane gargadi kan taruwa a cikin yanayin da ake ciki na annobar coronavirus.
A cikin wata sanarwar da NSCIA ta fitar a kan shafinta na Intanet, ta yi wa al'ummar Najeriya barka da ganin wannan lokacin na Sallah, tare da yi musu gargadi kan kiyaye ka'idojin da aka gindaya a lokacin sallar idi musamman a wuraren da aka cika sosai.
Kungiyar ta fadi hakan ne domin umartar mutane da su bi matakan da aka gindaya domin takaita yaduwar cutar COVID-19.
NSCIA ta kuma yi kira ga Musulmai wadanda suka yi niyyar zuwa aikin hajjin bana, wanda aka soke wa 'yan kasashen waje domin COVID-19 da su yi sadaka da kudaden hajjin.
A cewar kungiyar, yin hakan zai ba su lada daidai da wanda za su samu da sun je hajjin.
Shugaban kungiyar kuma mai martaba Sarkin Musulmi a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya jaddada yadda lokacin da aka ciki a matsayin mai cike da sarkakkiya.
"Dole mu kaucewa abubuwan da muka saba kamar sallah tare da mutane da dama domin yanayin da muke ciki."
A cikin makon da ya gabata hukumar alhazan Najeriya ta bayyana cewa za ta fara karbar kudaden aikin Hajji na badi.
Lamarin ya faranta wa 'yan Najeriya da dama rai, musamman wadanda suka yi niyyar zuwa aikin a bana.