Bayanai sun nuna cewa Kocin Super Eagle Salisu Yusuf wanda Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya ta dakatar da shi saboda rawar da ya taka a badakalar cin hanci, zai koma matsayinsa na Shugaban Kocin Super Eagles.
Idan za a iya tunawa dai a shekarar 2018 ne, aka samu Salisu da laifin karbar wasu kudade da aka ce yawansu ya kusan dala dubu daya.
Bayan nan Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya wato NFF, ta sanya masa takunkumi, sanan aka ci tararsa dalar Amurka dubu biyar $ 5000 da kuma dakatar da shi har na tsawon shekara guda daga ayyukan da suka shafi kwallon kafa.
Kafin a dakatar da shi, tsohon kocin Kano Pillars da Enyimba FC, kuma yake kula da kungiyar wasan matasa ‘yan kasa da shekaru ashirin da uku U-23, watau Olympic Eagles.
Bayan dakatarwar da aka yi masa, an baiwa Imama Amapakabo, damar ci gaba da kula da kungiyar Super Eagles da kuma na Olympic Eagles.
Sanarwar ta NFF ta ce "Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya ta lura da cewar babban mai horar da ‘yan wasan na Super Eagles, Salisu Yusuf ya kammala shekara daya na dakatarwa da aka bashi a shekarar da ta gabata.
"Kungiyar ta gode wa Koci Imama Amapakabo saboda kokarin da yake yi na horas da kungiyar yayin da yake jagorantar kungiyar ta ‘yan kasa da shekaru U23, lokacin da aka dakatar da Yusuf, kuma daga karshe ya jagoranci kungiyar zuwa shiga gasar cin kofin Afrika ta AFCON."