Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, dan kasar Masar Muhammad Salah, yayi tsokaci dangane da kalaman tsohon maihoras da Arsenal Arsene Wenger yayi akansa.
Salah ya bayyana cewa shahararrun ‘yan wasannan kwallon kafa a duniya guda biyu, wato Messi da Cristiano Ronaldo sunyi masa nisan da ba zai iya kamo suba.
A kwanannan ne cikin satin da ya gabata tsohon mai horar da kungiyar ta Arsenal, Arsene Wenger ya ce har yanzu Muhammad Salah, na da cikakkiyar damar kamo takwarorinsa Cristiano Ronaldo na Juventus, da kuma Lionel Messi na Barcelona, matukar ya cire son rai ya kuma ci
gaba da zura kwallaye kamar yadda ya faro a farkon kakar wasansa a Liverpool.
Wenger ya ce babu shakka kwazon dan wasan ya yi baya sosai, bayan da ya fara nuna son kai wajen ganin lallai duk kwallon da ya dakko shi zai sha da kansa, maimakon ya mika ga wani, a cewar tsohon kocin hakan babbar koma baya ne ga ‘yan wasa.
Sai dai a nasa bangaren Muhammad Salah, yace Ronaldo da Messi ‘yan wasane wadanda suka dade suna buga wasa a matakin manyan ‘yan
kwallo, kuma har yanzu tauraruwarsu tana haskawa a duniya saboda haka har yanzu bai kai matsayinsu ba.