WASHINGTON D.C. —
'Yan wasan Liverpool biyu, wato da Sadio Mane da Mohamed Salah suna cikin jerin ‘yan takarar da ka iya cin kyautar gwarzon ‘yan kwallon Afurka na bana.
Kyaftin din Riyad Mahrez na Aljeriya, wanda ke taka leda a gasar Zakarun Ingila, Manchester City na cikin jerin 'yan wasan.
Mane da Salah su ne suka fi dacewa da kyautar, bayan sun taimaka wa Liverpool ta lashe Kofin Zakarun Turai na UEFA, da European Super Cup da na kofin FIFA Club World Cup.
Mahrez, ya lashe kofin gida tare da kungiyarsa ta English sannan kuma ya rike shugabancin klub din Aljeriya a gasar cin kofin kasashen Afurka a watan Yuli, bayan da suka doke Senegal a wasan karshe.