Mai rike da gwarzon dan wasan kwallon kafa na nahiyar Afrika dan kasar Masar me taka leda a kungiyar Liverpool, Mohamed Salah yace ya shirya tsaf don sake lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Afrika karo na biyu a jere.
Gagarumin bukin zaben gwarzon shekarar zai gudana ne a kasar Senegal a ranar Talata 8/1/2019.
Mohammad Salah zai yi takarar lashe kyautar ne da takwararsa na Liverpool, Sadio Mane dan kasar Senegal da kuma Pierre - Emerick Aubameyang dan asalin Gabon da ke taka ledarsa a kulob din Arsenal.
A kakar wasan shekarar 2017/2018, Salah ya zurara kwallaye 44, a wasanni
daban daban da ya buga wa Liverpool, ya kuma taimaka wa kasarsa ta Masar ta samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya na 2018, da aka kammala a kasar Rasha.
Idan har dan wasan ya sake lashe kyautar a bana Salah zai kasance dan wasa na farko daga Arewacin Afrika da daya lashe kyautar sau biyu a jere.
Hukumar kula da kwallon kafa ta kasashen Afrika (CAF) take bada kyautar duk karshen shekara tun daga shekara ta 1990.
Haka kuma a ranar Talatar ne kuma hukumar kwallon kafar ta Afrika za ta zabi kasa daya tsakanin Masar da Afrika ta Kudu, don ba ta damar karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afrika na shekara 2019.
Hukumar ta janye izinin gudanar da gasar daga hannun kasar Kamaru a cikin watan Nuwamba 2018, saboda rashin kammala tanade-tanaden gasar da kuma barazanar tsaro a kasar ta Kamaru.
Mohammad Salah ya shiga wasan da Wolverhampton ta doke Liverpool 2-1, ranar Litinin dan wasan ya shiga fili cikin minti na 70, da ya canji Curtis Jones, rashin nasarra ya kawo sanadiyar cireta a gasar cin kofin kalu bale na kasar Ingila a bana, sai dai kuma Liverpool tana saman teburin firimiya lig mako na 21, da tazarar maki 4 tsakanita da Manchester City dake matsayi na biyu.