Sakon Shugaban Najeriya Ga Iyayen 'Yan Matan Dapchi

Dawowar Shugaba Mohammadu Buhari Daga Birnin London

Shugaba Buhari ya aika da sakon alhini ga iyayen 'daliban da aka sace a garin Dapchi.

A wani sako da ya kafe ta shafinsa na Twitter shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya tabbatarwa da iyayen ‘daliban da aka sace a garin Dapchi gwamnati na yin iya bakin kokarinta na ganin an gano inda yaran suke.

Sakon da Shugaban ya kafe na cewa “Ina son duk iyayen yaran da aka sace a makarantar sakandaren 'yan mata ta garin Dapchi su sani cewa, ana amfani da duk hanyoyin da ake da su wajen ganin an dawo da yaran cikin koshin lafiya, da kuma hukunta duk wadanda ke da hannu.

Daukacin mutanen Najeriya suna yiwa iyayen yaran da gwamnati da sauran mutanen Yobe alhinin faruwar wannan lamari. Wannan wani abune da ya shafi kasa baki daya. Muna mai baku hakurin faruwar wannan abu, kuma muna tare da ku. Ina mai tabbatar da cewa dakarunmu za su nemo duk yaran da suka bace.

Tuni dai aka baza sojoji aikin nemansu, kuma yanzu haka za a aika da karin sojoji da jiragen sama domin saka ido kan abubuwan da ke faruwa a yankin babu dare ba rana.