Sakon Kirsimeti: Paparoma Ya Yi Tir Da Halin Da Ake Ciki A Gaza, Ukraine Da Sudan

A gaban dubban mabiya darikar da suka yi dafifi a kofar majami'ar St. Peter’s Basilica dake birnin Rome, Paparoman ya kuma bukaci samun tsagaita wuta a Gaza da sakin Yahudawan da kungiyar Hamas ke garkuwa dasu a can.

A yau Laraba, a cikin jawabinsa na ranar Kirsimeti, Paparoma Francis ya bukaci a tsagaita wuta a fadin duniya, inda ya yi rokon samun zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya da kasashen Ukraine da Sudan sannan ya yi alwadai da mummunan yanayin agajin da ake ciki a Zirin Gaza.

Ya yi amfani da sakonsa na al'ada ga mabiya darikar Katolika biliyan 1.4 dake fadin duniya wajen yin kira domin samun tattaunawar sulhu a Ukraine a dai dai lokacin da rasha ta yiwa kasar ruwan makamai masu linzami da jirage marasa matuka 170 da safiyar ranar Kirsimeti.

A gaban dubban mabiya darikar da suka yi dafifi a kofar majami'ar St. Peter’s Basilica dake birnin Rome, Paparoman ya kuma bukaci samun tsagaita wuta a Gaza da sakin Yahudawan da kungiyar Hamas ke garkuwa dasu a can.

Paparoma Francis ya kuma fadada kiran nasa zuwa ga tsagaita wuta a ilahirin yankin Gabas ta Tsakiya da kasar Sudan, wacce kazamin yakin basasar watanni 20 ya daidaita tare da jefa milyoyin al'umnarta cikin barazanar yunwa