Sakataren Tsaron Amurka Chuck Hagel Yayi Murabus.

Shugaba Obama da sakatare Hagel mai murabus.

Shugaba Obama yace tun watan jiya sakatrae Hagel ya shaida masa cewa yana shirin yin murabus

Sakataren tsaron Amirka Chuck Hagel yayi murabus, bayan yayi kusan shekaru biyu akan wannan mukami.

Da yake magana a fadar White Houseyau litinin shugaba Barack Obama, da mataimakinsa Joe Biden yana tsaye kusa dashi, shugaban yace tun a watan jiya sakataren tsaron ya gaya masa cewa yana ganin lokaci yayi daya kamata yayi murabus daga kan wannan mukami.

Shi dai Mr Hagel, shine kadai dan jam'iyar Republican da ya rage majalisar Ministocin shugaba Obama. Yace zai ci gaba da kasancewa akan mukamin, har zuwa lokacinda aka nada wanda ko kuma wacce zata gaje shi.

Tun da farko, a yau Litinin jaridar The New York Times ta ambaci wasu manyan jami'an gwamnati suna fadin cewa Mr Hagel yayi murabus ne a saboda matsin lamba, a yayinda kasar ke fama da rikice rikicen akan manufofinta a kasashen waje, ciki harda fafatawar da Amirka ke yi da yan kungiyar ISIS a Syria da Iraq.

Mr Hagel shine jami'in gwamnati na farko da yayi murabus, tun lokacinda jam'iyar Republican ta lashe zabe a farkon wannan watan. Jam'iyar Republican ce zata kasance mai rinjayen wakilai a Majalisar dokoki a watan Janairu.