Baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon yace rashin ya baci sosai da ya ji labarin cewa an gano gawarwarkin yan gudun hijira saba'in da daya cikin wata babar mota akan wata babar hanya a kasar Austria kusa da kan iyakar kasar Hungary.
Yawancin gawarwarkin da yan kasar Syria ne, ciki harda yara, wadanda suke kokarin arcewa yaki da ta'adanci, domin neman inganta rayuwar su a turai,
Jiya Juma'a Mr Ban yace yakin da ake yi a Syria da baiyana a gefen hanya a tsakiyar turai
Haka kuma Mr Ban yayi Allah wadai da masu fasa kaurin mutane da mutane da ke yin somagal din mutane suna yin watsi da yan gudun hijira akan teku suna barin ruwa na cinye su. Ya baiyana tekun Meditereniyan a zaman inda ake ko kuma tarkon mutuwa.
Akalla mutane uku aka kama bayan da aka gano gawarwarkin a ranar Alhamis akan wata hanya a kasar Austria. 'Yan sanda sunce sunyi imanin cewa yawancin mutanen da suka mutu, sun rasu ne a saboda rashin isasshen iska.
Baya ga ganin cewa sun cika alkawarun da suka dauka na baiwa yan gudun hijirar da suke arcewa hatsari kariya da mafaka, Mr. Ban yace tilas kasashen duniya su kara zage dantse wajen magance rikice rikice da wasu matsalolin da suke tilastawa mutane arcewa domin basu da zabi. Mr Ban yace kasa yin haka zai sa fiye da yan gudu hijira dubu arba'in da aka samu a kullu yaumin karuwa.
Yawancin yan gudun hijirar suka arcewa ne daga kasashen Syria da Iraq da kuma Afghanistan
Baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon yace rashin ya baci sosai da ya ji labarin cewa an gano gawarwarkin yan gudun hijira saba'in da daya cikin wata babar mota akan wata babar hanya a kasar Austria kusa da kan iyakar kasar Hungary.