Sakataren JNI Ya Ce Musulunci Ya Haramta Cin Zarafin Yara

Taron Jama'atul Nasir Islam reshen jihar Filato akan kawo karshen cin zarafin yara

Kungiyar Jama'atul Nasir Islam da hadin gwuiwar hukumar Majalisar Dinkin Duniya dake kula da yara sun shirya taron kawo karshen cin zrafin yara da bincike ya nuna cewa kashi sittin na yaran Najeriya ne ake cin zarafinsu kafin su cika shekaru 18 da haihuwa

Sakataren kungiyar Jama'atul Nasir Islam reshen Filato, Shaikh Khali Aliyu ya ce akwai mummunan sakamako ga duk wanda ya ci zarafin yara ta hanyar tauye masu hakkokinsu wajen hanasu abinci, azabtar dasu, cusa masu tsoro da fargaba da nuna masu wariya.

Ya ce "Musulunci ya yi Allah wadai ya kuma bakanta duk wani aiki da yake da alaka da cin zarafin yara".

Akan almajiran da akan gansu suna gararamba akan tituna, Shaikh Aliyu ya ce "shi ma wannan ba Musulunci ba ne" Ya ce mummunar al'ada ce ta shiga cikin abun. Injishi ba aiki ba ne amma abu ne na neman ilimi aka karkatar dashi ta wata hanya daban.

A cewar Shaikh Aliyu an kafa wani kwamiti mai karfi da zai yi maganin lamarin. Ya kara da cewa lallai iyaye su ji tsoron Allah. Duk wanda ya bar dansa na gararamba akan titi Allah ba zai barshi ba.

Ita ma wakiliyar shugabar hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya dake da ofishi a Bauchi, Ladi Alabi, ta ce bincike ya nuna cewa akwai yawaitar cin zarafin yara a Najeriya. Ta ce yara shida cikin goma kan fuskanci cin zarafi ta hanyar azabtarwa , fyade ko wani tashin hankali kafin su cika shekaru goma sha takwas.

A saurari rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Sakataren JNI Ya Ce Musulunci Ya Haramta Cin Zarafin Yara - 3' 14"