Sakataren Harkokin Wajen Amurka Zai Gana Da Jami'an Japan

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, ya na Japan zangonsa na farko a rangadin da yake yi a Asiya, da aka shirya domin kara tabbatarwa kawayen Amurka, zai kuma gudanar da shawarwari kan hanyoyin shawo barazanar Nukiliya da makamai masu linzami daga Koriya ta Arewa.

Yayin da sakataren yake wannan balaguro domin ganawa da jami'ai a Japan da Koriya ta kudu da China, ba zai tafi da tawagar wakilai daga kafofin yada labarai da suka saba tafiya da shi, maimakon haka ma'aikatar ta zabi wakili daya, daga wata mujalla a internet mai ra'ayin 'yan rikau shi kadai ne zai raka shi.

Da farko ma'aikatar harkokin wajen tace an dauki matakin ne domin jirgin da sakataren Tillerson zai yi tafiyar da shi karami ne, amma daga karshe ya tafi da Beoing 737 wadda zai iya daukar wakilai da ya saba tafiya da su.

Yau Alhamis ake sa ran sakataren zai gana da PM Japan Shinzo Abe, da kuma ministan harkokin waje Fumio Kishida.

Gobe Jumma'a ake sa ran zai gudanar da shawarwari mukaddashin shugaban Koriya ta kudu da kuma minista harkokin wajen kasar, amma babu shirin zai gana da shugabannin 'yan hamayya.