Sakamakon Zaben Yan Majalisun Tarayya Na Kano Da Jigawa

An Kama Wani ‘Dan Jam’iyyar APC Da Katunan Zabe Fiye Da 300 A Jihar Kano

Turawan zabe a Najeriya na ci gaba da bayyana sakamakon zabe a matakin kasa da jihohi da kuma mazabun ‘yan majalisar dokokin Kasar.

A jihohin Kano da Jigawa, an bayyana sakamakon zaben kujerun ‘yan majalisar tarayya da na jihohi.

Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi babban baturen zabe na jihar Jigawa shine ya bayyana sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Jigawa a shalkwatar hukumar da ke Dutse.

Bayan bayyana jimlar mutanen da suka karbi katin zabe a jihar, farfesa Armaya’u ya kuma sanar da adadin wadanda aka tantance domin kada kuri’a, kana daga bisani ya bayyana yawan kuri’un da ‘yan takarar kowace jam’iyya suka samu.

Ya ce Jam’iyyar APC ta sami kuri’u 421,390, yayin da Jam’iyyar PDP take da 386,587.

A kujerun ‘yan Majalisar Dattawa kuwa a jihar ta Jigawa, jam’iyyar APC ta lashe kujeru biyu yayin da PDP ta samu kujera daya.

A jihar Kano kuma, an tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 40 daga cikin 44 na jihar kamar yadda bayanai daga cibiyar tattara sakamakon zabe dake shalkwatar hukumar INEC suka nuna.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, sakamakon ‘yan majalisar dattawa ya nuna jam’iyyar APC ta yi nasara a mazabar Kano ta arewa, yayin da jam’iyyar NNPP ta yi gabalaba a mazabar dan majalisar dattawa ta Kano ta kudu

Farfesa Aliyu Sulaiman Kantudu ya bayyana Garba Mohammed Diso na Jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe kujerar dan majalisar tarayya ta Gwale,

Sakamakon zabukan ‘yan Majalisar dattawa da sauran kujeru sun kammala da wuri a mazabar karamar hukumar Nasarawa, wadda ta yi kaurin suna wajen samun sarkakiyar zabe.

Bayan karanta sakamakon zaben, jami’in zabe na Majalisar Dattawa a karamar hukumar farfesa Umar Sani ya bayyana cewa, an yi zabe cikin lumana kuma sun sami hadin kai daga wakilan Jam’iyyu.

Your browser doesn’t support HTML5

Sakamakon Zaben Yan Majalisun Tarayya Na Kano Da Jigawa - 3'30"