Sakamakon Zaben Birtaniya Ya Gurgunta Firayim Minista Theresa May

Firayim Ministar Birtaniya Theresa May

Murna ta komawa Theresa May Firayim Ministar Birtaniya ciki saboda sakamakon zaben da ta kira cikin gaggawa yayi mata bazata maimakon ta kara yawan 'yan majalisar da take dashi hasara ma tayi yayinda jam'iyyar Labour ta samu karin kujeru

Masu kada kuri’u a Birtaniya sun juyawa jam’iyyar masu ra’ayin rikau ta Firai Minista Theresa May baya, inda ta yi hasarar kujeru a zaben gaggawar da ta kira bisa kokarin karfafa goyon baya kafin fara tattaunawar ficewar Britaniya daga Tarayyar Turai.

Cacar da May tayi ta kiran zabe da gaggawa ta sa a yanzu jam’iyyarta ta rasa rinjayen da take da shi a cikin majalisar wakilan kasar kafin zaben.

Sakamakon zaben bai yiwa May dadi ba, wacce ta yi saurin kiran zaben cikin gaggawa shekaru uku kafin lokacin da aka saba yinsa, da burin samun karin goyon baya don karfafa hannun Birtaniya wajen fitar ta daga tarayyar turai. Ta fuskanci matsin lamba akan ta sauka daga kan mukamin ta na Firai Minista.

A bayan da aka samu sakamakon kujeru 636 daga cikin 650 na karamar majalisar, Jam’iyyar masu ra’ayin rikau na da kujeru 310 yayin da Jam’iyyar Labour ke da 258. Ko da kuwa jam’iyyar ta Conservative zata lashe sauran kujerun da ba a bayyana sakamakonsu ba, ba zata iya samun kujeru 326 da take bukata domin samun rinjaye a majalisar ba. Kafin zaben dai jam’iyyar firayim ministar tana da kujeru 330 yayin da Labour take da 229.

A bangaren canjin kudi kuwa, Fam na Birtaniya ya rasa kwabbai biyu akan Dalar Amurka yan dakiku bayan an bayyana alkaluman jin ra’ayi, kafin ta farfado shi.

Idan har an takura May ta sauka daga kan mukamin ta na Firai Minista, cikin watanni 11 da fara aiki a ofishinta, Lokacin ta zai kasance mafi kankanta a tarihin Firai Minstocin da a kayi a Birtaniya tun daga shekarar 1920.