Sakamakon Tashin Bamabamai A Kano

Mutane na gudu yayin da bam ya tarwatse (File photo)

Sakamakon tashin bamabamai a Kano mutane da dama ne suka rasa rayukansu wasu da yawa kuma suka jikata
Bamabamai hudu da suka tarwatse a Sabon-garin Kano sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama yayin da wasu suka jikata kamar yadda wakilinmu ya gano a zagayawar da ya yi.Ya zanta da wadanda abun ya faru a idanunsu.

Mutun na farko da ya zanta da shi a asibiti ya ce shi yana zaune ne a kan wani tebur sai ya ji fashewar wani abu yayin da shi kansa a ka daga shi sama ya fado da ka. Baraguzen bamabaman sun shiga cikin kafarsa yadda baya iya tafiya sai da aka daga shi. Yanzu yana jiran a yi masa tiyata a asibitin koyaswa na Malam Aminu Kano. Wani da ya tsallake rijiya da baya ya ce wajan karfe tara na dare suka ji kara sai kuma duhu ya biyo baya. Kafin ya farga sai ya ga gawarwaki a gabansa. Daga wurin ya ce suka fara gudu.

Hukumomi da kungiyoyin bada agaji tuni suka soma kai doki ba kama hannun yaro. Kungiyar agaji ta Red Cross ta zagaya inda ta dinga kwasan bangarorin jikin mutane ta kai asibitin koyaswa. Kodayake basu samu adadin wadanda suka mutu ba kakakin 'yansanda Musa Majiya ya ce mutane goma 12 suka rasu 12 kuma suka jikata. Amma a asibitin Malam Aminu daraktan hulda da jama'a na asibitin Alhaji Aminu Inuwa Ringim ya ce akwai gawarwaki 24 a wurinsu. Haka ma wata majiya a asibitin Murtala ta ce akwai gawarwaki 21 da wasu 11 dake karbar magani.

Tuni dai gwamnan jihar Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci wadanda lamarin ya shafa a asibitocin da suke tare da yin tur da wannan aika-aika. Ya ce gwamnati zata dauki nauyin biyan kudin jinyar mutanen dake kwance a asibitocin.

Mahmud Ibrahim Kwari nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Sakamakon Tashin Bamabamai A Kano - 3:25