Manya-Manyan jami'an tsaron kasar suka ce sakamakon bayanan sirrin da suka tattara ya nuna cewa kasar tana huskantar barazanar ta'addanci.
Shugabannin Jami'an tsaron sun bayyana hakan ne jiya Laraba,jim kadan bayan sun gama ganawa da shugaba John Mahama akan shirin da suke yi na tinkarar wannan babban kalubale.
A cikin sanarwar da suka bayar sun bukaci ‘yan kasar ta Ghana da su kula kuma sukai rahoton duk wani abu da suka gani kusa dasu da suke kwankwanto akan sa.
Wannan dai shine karo na farko da wata kasar Africa ta yamma zata zauna cikin shirin kota kwana.
Idan dai ba a manta ba a cikin watan Nuwanbar bara ne kungiyar Al Qaida takai hari a wasu otel-otel dake kasashen Mali da Bukina faso wato Bamako da Ouagadougou, sai kuma wanda suka kai a gabar teku inda mutane ke wankan shakatawa.
To sai dai duk da cewa gwamnati tace tana ciki shiri amma har yanzu wasu ‘yan kasar ta Ghana na cewa anya gwamnati da gaske take yi kuwa.