Sakaci da ko-in-kula ne masababin tashe tashen hankali a Najeriya-Kwankwaso

Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

Sakaci da rikon sakainar kashi da gwamnatin tarayya ke yiwa sha’anin tsaro shine musabbabin kai sabbin hare-hare a wasu sassan arrewacin najeriya, inji gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso

Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso yace sakaci da rikon sakainar kashi da gwamnatin tarayya ke yiwa sha’anin tsaro shine musabbabin kai sabbin hare-hare a wasu sassan arrewacin najeriya da kuma farmakin da aka kaiwa wasu fitattun mutane irin su Janar Muhammadu Buhari da kuma Sheikh Dahiru Usman Bauchi. A ganawa da manema labarai bayan ya dawo gida a karshen mako, daga balaguran da ya yi a kasashen waje gabanin kammala azumin watan Ramadan da ya gabata, gwamnan na Kano ya bayyana takaici kan yadda al’amuran tsaro ke kara sukurkucewa a Najeriya. Gwamna Kwankwaso yace ba a arewacin Najeriya kadai ake fama da matsalolin tsaro ba, bisa ga cewarshi, a wadansu sassan kasar ma, matsalolin tsaron sun sa tilas a rika rufe cibiyoyin kasuwanci da wuri domin gudun hare hare. Daga Kano ga rahotan da Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana.

Your browser doesn’t support HTML5

Martanin Kwankwaso kan harin Buhari