Kyaftin na 'yan wasan kwallon kafar kasar Ivory Coast, Didier Drogba, yace sai kasarsa tana dab da bugawa da Portugal a wasansu na farko wajen gasar Cin Kofin Duniya, zai yanke shawara a kan ko zai buga.
Dan wasan na kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea a Ingila mai shekaru 32 da haihuwa, ya karya wani kashi a hannunsa na dama a lokacin wasan tayar da tsimi na karshe da kasarsa ta yi da Japan ranar 4 ga watan Yuni a Switzerland. Yau litinin kwana biyu ke nan a jere Drogba yana halartar motsa jiki na kungiyar Ivory Coast a bayan da aka yi masa tiyata a hannun.
A bara, Drogba shi ne dan wasan da ya fi jefa kwallaye cikin raga a wasannin lig-lig na kasar Ingila.
Mai koyar da 'yan wasan Ivory Coast, Sven-Goran Eriksson, yace Drogba zai yanke shawara sa'o'i biyu kafin gwabzawar da kasar zata yi da Portugal talata a garin Port Elizabeth a Afirka ta Kudu.
Har ila yau, sai Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta duba ta kunma amince da Filasta da aka daure hannun Drogba da ita kafin a kyale shi ya buga. Hukumar zata nazarci filastar ce domin tabbatar da cewa ba zata zamo hatsari ga sauran 'yan wasa ba.
An bayyana wannan rukuni na 7 ko "G" inda kasar Ivory Coast take a zamanin rukunin mutuwa a gasar cin kofin Kwallon Duniya a bana a saboda karfin kasashen dake wannan rukuni. A bayan ita Ivory Coast akwai kasashen Brazil, da Portugal da kuma Koriya ta Arewa.