Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce sai an bi duk matakan tantancewa ne na tabbatar da kasancewar mutum dan kasa kafin yi ma sa rejista.
INEC kai tsaye ba ta yi magana kan kama wasu da a ka yi kwanannan 'yan kasashen waje a Ibadan da rejistar zabe ba, amma ta ce a bangaren ta, sai ta tantance ne ta kan yi wa mutum rejista.
Hukumar zaben wacce ta kammala zagaye na karshe na sabunta rejistar gabanin babban zaben 2023, ta baiyana filla-filla irin matakan da ta kan bi gabanin yin rejistar.
Jami'a a sashen labarun hukumar Zainab Aminu ta baiyana cewa har sai mutum ya zo da kofin shaida da za a gani kafin samun damar.
A zaben mai zuwa na ranar 25 ga Fabarairu da 11 ga Maris, hukumar ta ce za ta yi amfani da sabuwar na'ura mai taken BVAS da za ta tattara dukkan bayanai don hana duk kofar magudi.
Shugaba Buhari dai da zai kammala mulki bayan babban zaben ya tabbatar da wanda ya lashe zabe zai mikawa ragama.
Masanin harkokin siyasa a Abuja Dr.Farouk BB Farouk ya aza shugaban a kan faifai da hasashen cewa ba zai tallafawa kowane bangare ba a siyasance.
Yayin da APC ke fatan zarcewa kan mulki jam'iyyun adawa na gwagwarmayar amshe madafu daga kammala wa'adin shugaba Buhari.
In za a tuna daga dawowa dimokradiyyar a 1999, PDP da ke zaman babbar jam’iyyar adawa yanzu ta yi mulkin tsawon shekaru 16 inda a 2015 gamaiyar jam’iyyun adawa da su ka dunkule karkashin shugaba Buhari su ka amshe ragama.
Za a jira a ga wanda zai kai labari a babban zaben da hasashe ke nuna komai ka iya faruwa kuma kai tsaye ba za a iya cewa ga lalle mai tagomashin lashe zaben ba.
PICS-Wasu 'yan takarar gwamna a zauren VOA, gangamin magoya bayan jam’iyyar gwamnati a Abuja da gangamin 'yan jam'iyyar adawa a Abuja.
Saurare cikakken rahoton cikin sauti
Your browser doesn’t support HTML5