Sai An Tantance Kayan Da Jarumi Zai Sa A Kowane Wasa - Mustapha Usman

Harkar bada kaya a masana’antar Kannywood wato Costume, za’a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu, in ji Mustapha Usman, mai sana’ar Costume, wato shirya jarumai, duba da ganin irin dadewar da yi a masana’antar tare da la’akari da irin nasarorin da fina-finan da ya fitar masu da kaya suka yi.

Ya ce a duk fim din da za’a fitar ana fara basu script na fim su fara karantawa domin fitar da kayan da jarumai ya kamata su sanya sannan zai taimaka wa Costumer, wato mai bada kayan sanin irin kayan da ya dace a sakawa jarumi na birni ne ko na kauye.

Ya kara da cewa su dai wadannan kayayyaki a mafi yawan lokuta saye ake yi sannan da zarar an kammala fim kayan sun tashi daga aiki sai dai a sayar ko kuwa mai fim ya san me zai yi da su.

Ku Duba Wannan Ma Mahaifiyar Jaruma Nafisa Abdullahi Ta Rasu

Mustatpha, ya ce kimanin shekaru goma Kenan yana harkar Costumer sannan ya na dada gogewa a fannin bada kaya ta hanyar wasu tarurrukan karawa juna sani domin inganta sana’ar.

Ko da yake ya ce bai taba fuskantar wata matsalar bada kayan da basu dace ba a fina-finan da ya fitar da kaya kuma babban burinsa a rayuwa shi ne masana’antar Kannywood ta bunkasa.

Your browser doesn’t support HTML5

Sai An Tantance Kayan Da Jarumi Zai Sa A Kowane Wasa - Mustapha Usman