Sadio Mane Zai Sabunta Kwantirakinsa

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool dan kasar Senegal Sadio Mane, ya amince da zai sabunta kwantirakinsa a Anfield, zuwa wani dogon lokaci.

Mane mai shekaru 26 da haihuwa, ya koma Liverpool daga kulob din Southampton a shekara ta 2016 cikin watan Yuni akan kudi fam miliyan 34 a yarjejeniyar shekaru biyar.

Ya zuwa yanzu, dan wasan ya buga wasannin 86 wa Liverpool a dukkannin gasar da ta yi ya samu nasarar zura kwallaye har guda 40 a raga, ya taimaka mata a gasar cin kofin zakarun turai 2017/18, inda Liverpool ta kai wasan karshe.

Ku Duba Wannan Ma Dan Wasan Chelsea Didier Drogba Na Shirin Ritaya Daga Murza Leda

An sanya sunan dan wasan cikin jerin sunayen 'yan wasa 30 wanda za'a zaba gwarzon zakaran kwallon kafa na duniya 2018, haka kuma yana daga cikin 'yanwasa da zasu kara na neman zakaran kwallon kafa na Nahiyar Afirka, wanda BBC take zaba.

Mane ya ce ya yi matukar farin ciki da ya kasance zai kara tsawaita kwantirakinsa a wannan kungiya, kuma wannan rana ce mai mahimmanci a gare ni, na kuma yanke shawaran ci gaba da zama a Liverpool hakan shi ne mafi kyau a wajena.

Sabon kwantirakin dan wasan zata kare a shekara ta 2023, ya yi alkawarin taimakawa kungiyar ta Liverpool wajan samun nasara a dukkannin wasannin ta na gida da waje.

Mane yana cikin tawagar kungiyar kwallon kafa na kasar Senegal da suka fafata a gasar cin kofin duniya da ya gabata a 2018, inda ya jefa kwallo daya a raga a wasannin uku da suka yi.