Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa na Liverpool, dan kasar Senegal, Sadio Mane mai shekaru 25, da haihuwa zai tafi jinya na tsawon makwanni shida, sakamakon raunin da ya samu a kafarsa.
Dan wasan ya samu wannan raunin ne a cikin minti na 85, a wasan da kasarsa ta Senegal, tayi tsakaninta da kasar Cape Verde, a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na shekara 2018, da za'ayi a kasar Rasha. Inda Senegal tabi Cape Verde gida ta doketa daci 2-0.
Sakamakon wannan rauni da ya samu Sadio Mane, ba zai samu damar fafatawa a wasan da kungiyarsa ta Liverpool, zatayi da Manchester United, ba a gasar firimiya lig na bana mako na tara ranar Asabar da kuma wasan cin kofin zakarun nahiyar turai ba wanda zasu kara da kungiyar Maribor.
Haka kuma dan wasan bazai samu daman taka leda a babban wasan da kasarsa ta Senegal, zatayi da kasar Afirka ta kudu ba a cigaba da wasannin neman gurbin wasan cin kofin kwallon kafa na duniya, a matakin wasan rukuni, Senegal, dai ta na matsayi na daya ne a rukunin (D) da maki 8.
Mane ya jefa kwallaye guda uku a wasannin biyar da ya buga wa kungiyarsa ta Liverpool, a bangaren firimiya lig na bana a kasar Ingila.
Inda a wasan da suka buga da kungiyar Manchester City, wanda aka doke Liverpool, kwallaye 5-0 a gasar Firimiya lig mako na biyar an dakatar da dan wasan na tsawon wasanni uku, sakamakon laifi da dan wasan yayi.
Your browser doesn’t support HTML5