Sabuwar Rundunar Soji A Arewa Maso Gabashin Najeriya

Sojoji masu tsaro

Najeriya ta kafa sabuwar rundunar soji a arewa maso gabashin Najeriya a kokarinta na kawo karshen duk wani aiki da barazanar ta'adanci.
Gwamnatin Najeriya ta kafa sabuwar rundunar soji da ta kunshi mayakan sama da na kasa da na ruwa da ma wasu jami'an tsaro a wani hadi na musamman.

Yayin da yake jawabi ga wannan sabuwar rundunar yaki da masu tada kayar baya babban hafsan hafsoshin sojin mayakan sama Air Vice Marshall Alex Badeh ya gargadesu da su kara daura damarar yaki da wadanda ya kira 'yan ta'ada. Ya ce wadanda ke kai mana hari ba dukansu bane 'yan Najeriya. Akwai mutanen kasashen waje cikinsu. Akwai masu taimaka masu da kudi da kayan yaki daga kasashen waje. Akwai masu turo masu da makamai daga waje.

Yanzu haka hukumomi a jihar Adamawa na cigaba da fadakar da jama'a game da aikin sabuwar rundunar wadda ke da hekwata aYola, musamman mutanen dake kan iyakar Najeriya da wasu kasashe. Kwamishanan Iyaka Alhaji Hamza Bello ya kirawo mutanen dake iyaka da su hada kai da jami'an tsaro da aka turo zuwa jihar ta Adamawa domin a cimma nasara kamar yadda gwamnan jihar ya riga ya bayyana. Can baya gwamnan ya fada cewa mutanen Adamawa masu son zaman lafiya ne masu kuma son cigaban kasar.

Ga karin bayani daga Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Sabuwar Rundunar Soji A Arewa Maso Gabashin Najeriya-3.17