Sabuwar Na'urar Alexa Zata Taya Mutane Hira Kamar Mutum

Kamfanin Amazon ya bayyanar da wasu daga cikin sababbin tsare-tsare da ya kammala don inganta nau’arar Alexa, wadda ke taimakon jama’a wajen kunnawa da kashe duk wasu na'urorin zamani da suka hada da talabijin, AC, fanka, radiyo da dai sauransu a gidajensu.

Na'urar Alexa da kamfanin na Amazon ya kirkira tare da hadin gwiwar kamfanin Google, mutane na iya magana da ita don samun bayanan abubuwa da dama a duniya. Yanzu haka kamfanin ya inganta na’urar, ta yadda mutane zasu dinga fira da ita kamar yadda ake fira da mutane.

Abu da mutun ke bukata shine ya hada na’urar da yanar gizo, sai mutum ya saka lasifika a kowace kusurwa ta gidan shi, a duk lokacin da yake so yayi fira kawai, zai yi magana ita kuwa na’urar zata amsa mishi dai-dai da abun da ya tambaye ta, kana mutum na iya tambayar ta ta bashi wani labari.