A makon da ya gabata ne shugaban kasar Nijar ya kaddamar da ayyukan sabuwar makarantar horas da hafsoshin sojan kasar, a ci gaba da kara jan damarar yakin da kasar ke yi da ‘yan ta’adda. Mohamed Bazoum ya ce zai dauki matakin rubanya yawan dakarun kasar a shekarun dake tafe, a don haka za a bude wasu makarantun sojan sama da na sojan kasa a Agadez da Keita. Ga Yusuf Abdoulaye da rahoton daga Niamey.
Sabuwar Makarantar Horar Da Sojoji Da Aka Bude A Jamhuriyar Nijar
Your browser doesn’t support HTML5
Wannan na zuwa ne yayin da kasar ta Jamhuriyar Nijar ta kara damarar yaki da ayyukan ta'addanci a kasar.