Ofishin sabon shugaban kasar Koriya ta kudu Moon Jae-In ya fada yau Alhamis cewa shugaban na shirin tura wata tawagar wakilansa China don tattaunawa akan shirin Nukiliyar Koriya Ta Arewa da kuma damuwar China akan makami mai linzami na kariya da Amurka ta girke a Koriya Ta Kudu.
Wani mai magana da yawun shugaba Moon yace shugabannin sun amince akan bukatar kawar da duk wasu makaman nukiliya a yankin Koriyoyin biyu, kuma Moon ya gamsu da damuwar China akan makamin kariyar THAAD da Amurka ta girke.
China dai na ganin wannan makamin na THAAD a matsayin wata barazana ga ita kanta, wanda kuma zai iya bata zaman lafiyar yankin da ake ta yiwa cin kwan makauniya. Sannan tuni ta mayar da martani ta hanyar takaita shiga da kayayyaki daga Koriya ta Kudu da ma masu yawon bude ido.