Sabon Mai Yada Labarai Na Fadar White House Na Mayar Da Martani

Belarus - US president Donald Trump, Czech Republic president Milos Zeman, combo

Yanzu dai ta fito fili an samu barakar da bata boyuwa a gwamnatin Shugaba Donald Trump abinda yasa sabon mai kula da harkokin yada labarai yake caccakar masu fallasa gwamnatin

Barakar da ake samu a Fadar shugaban Amurka ta White House, ta fito baina jama’a, yayin da sabon shugaban da ke kula da sashen yada labarai, Anthony Scaramuchi, ya fara caccakar wadanda ke kwarmata bayanan abin kunyar da ke faruwa ga gwamnatin shugaba Trump, inda cikin kakkausar murya, ya kaddamar da yakin tunkarar abokanan hamayyarsa da ke Fadar ta White.
Scaramuchi ya caccaki shugaban ma’aikatan Fadar ta White House Rience Priebus da kuma shugaban tsare-tsaren dabaru, Steve Bannon, inda ya yi amfani da wasu kalaman batsa a wata hira da jaridar “The New Yorker” da ke fitowa mako-mako, wacce ta wallafa a shafinta na yanar gizo a jiya Alhamis.
Scaramuchi, wanda hamshakin mai kudi ne da ya taba aikin banki a yankin hada-hadar kasuwanci na Wall Street, wanda kuma dan gani-kashenin shugaba Trump ne, ya fara caccakar Priebus ne, wanda yake zargi da kwarmata bayanan sirrin da aka tattauna a tarukan Fadar White House.
Priebus, wanda shine tsohon shugaban jam’iyar Republican, na da alaka ta kut-da-kut da gaggan ‘yan jami’iyar Republican da ke majalisar dokokin Amurka, kuma jigo ne a cikin jami’an gwamnatin ta Trump.
A wata hira da suka yi ta wayar talho, Scaramuchi ya fadawa wakilin jaridar ta The New Yorker a Washington cewa “Rience dan-abu-kazan-abu-kaza-ne, wanda a koda yaushe, yake fama da matsalar nan da mutum yake tunanin wasu na kulla wata makarkashiya akansa.