Kamfanoni da dama masu kera motocin zamani na ci gaba da lalubo hanyoyin inganta motoci masu sarrafa kansu. Shi kuwa wani kamfanin kasar Australia tare da hadin gwiwar takwaransa na kasar China, sun fara gwajin wani jirgi mai saukar angulu na haya a karon farko.
Jirgin na dauke da farfeloli 16 kana yana da nauyin kilogram 340 kg, wanda ya fara sauka a filin wasanni na kasar ta Australia, jirgin yayi shawagi na wasu mintuna kafin daga bisani ya sauka.
Jirgin mai suna EHang mai daukar mutane 2, an gwada shi matuka da kuma tabbatar da cewar ya cika duk wasu ka’idoji da ake bukatar jirgin mai shawagi a sama ya cika, a cewar shugaban kamfanin Derrick Xiong. Ya kuma kara da cewar yanzu haka kamfanin ya shirya tsab don wadatar da jiragen ga ‘yan kasuwa.
Jirgin dai zai iya tafiya a sararin samaniya har nisan kimanin kilomita 150 cikin sa’a daya, kuma zai iya tafiya da ta kai nisan kilomita 50 zuwa 70.
Shugaba ya ce yanzu haka mutane har sun fara biyan kudin su don sayen jirigin da kudin shi ya kai kimanin dalar Amurka $336,000 dai-dai da naira miliyan dari da ashirin.