Sabon Rikicin Kabilanci Ya Barke A Arewacin Kenya

Garin Moyale a arewacin kasar Kenya.

Gap da lokacin da gwamnatin kasar Kenya ke tara dakarun da zata tura arewacin kasar sai ga shi sabon rikicin kabilanci ya barke a yankin
Jami'an kasar Kenya da ma'aikatan agaji sun ambato barkewar sabon rikici tsakanin kungiyoyin kabilu masu gaba da juna a arewacin kasar ranar Asabar, kwana biyu bayan gwamnati ta yi kokarin tura dakarunta a yankin dake fama da rikici.

Jami'an sun ce an kashe mutane da dama a sabon fadan da ya sake barkewa ranar Asabar kusa da garin Moyale. Fadan da aka ta gwabzawa tun makon jiya ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama kana wasu 1000 tuni suka tsallaka iya suka shiga kasar Habasha.

Rikicin ya samo asali ne daga takardama kan filayen kiwo tsakanin kabilu makiyaya dake gaba da juna.

Amma zaman tankiya tsakanin kabilar Borama mafi rinjaye da sauran kabilun ya kara yin tsamari cikin 'yan kwanakin nan.

Ranar Juma'a gwamnati ta ce zata tura dakarunta yankin domin mayar da doka da oda da zaman lafiya. Sai dai kawo yanzu gwamnati bata kayyade yawan dakarun da zata tura ba.