Sabon Haraji Kan Kamfanonin Tabar Sigari Da Barasa Ya Fara Aiki A Najeriya

Mental Health Smoking

Gwamnatin Najeriya ta fara aiki da sabon haraji da ta saka wa kamfanonin tabar sigari da na barasa abin da kuma ke samun martani daga jama'ar kasar.

A watan da ya gabata ne Ministan kudi, Kemi Adeosun ta bayyana cewa Shugaba Buhari ya amince da haraji ga kamfanonin da ke sarrafa tabar sigari da kuma barasa, kuma za a kwashe shekaru uku ana karban harajin wato daga 2018 zuwa 2020.

Hakan zai bai wa hukumomi damar daidaita farashin sigari da kuma barasa tare da samun kudaden shiga da gwamnatin tarayyar Najeriya ke nema bayan wanda take samu daga man fetur da sauran kayayyakin da ta ke fitarwa na gona.

A karkashin wannan sabon tsarin harajin da aka kakabawa kamfanonin, za a kara Naira daya akan kowane karan sigari abin da ke nuna Naira 20 kenan akan kowane kwalin sigari mai kara 20. A shekarar 2019, za a samu karin Naira biyu wanda zai kai ga Naira 40 akan kowane kwalin sigari mai kara 20 har zuwa 2020 da harajin zai kai kusan Naira biyu da kobo casa'in a kowane kara wato dai Naira 58 kenan akan kowane kwalin sigari.

Wani mai sayar da sigari ya ce lallai farashin tabar sigari zai karu kuma duk da cewa mai yiwuwa jama'a za su rage sayanta, wannan abin farin ciki ne.

"Muna farin ciki a daina shanta wallahi. Inda Allah zai sa ta kai kara daya Naira 50, mu muna fatan hakan. Saboda gaskiya asarar da ake yi ta lafiya ta yi yawa musamman nan Legas, shan sigari ta yi yawa."

Wani mai shan sigari cewa ya yi, "Mun ji labarin karin farashin kuma muna ganin muma zai taimaka mana wajen kaurace wa shan sigarin tun da ba abu ba ne da ke kara lafiya ba. A koyaushe fatanmu shi ne, mu bar shan sigari."

Saurari rohoton Babangida Jibril

Your browser doesn’t support HTML5

Sabon Haraji Kan Kamfanonin Tabar Sigari Da Barasa A Najeriya - 3' 52"